Header Ads Widget

KALAMAN SOYAYYA TEXT MESSAGES

 Kalaman Soyayya Text Messages

Dafatan kintashi lafiya, jiya ina cikin damuwa, amma ganin ki ya kawar mun da duk damuwar dake zuciya ta. Ya rayuwa ta zata kasance ba tare da ke ba? Gaskiya nayi sa’ar samun ki a rayuwa ta.


Da zaki iya ganin irin halittar da ubangiji yayi maki, da kin gane cewa ke ta daban ce a cikin yammata hadaddu. Kyawun ki ba irin tasu ba ce.

Karanta: YADDA AKE MALLAKE USTAZIYA

Na fada maki wani abu da baki sani ba? Kina da maganin dake magance wata cuta da nake fama da ita. Murmushin ki ita ce maganin kuma wannan cutar ita ce damuwa. Duk inna shiga damuwa, murmushin ki kawai nasa na manta da damuwa dana ke ciki.


Gabanin sanin ki, bansan mene ake nufi da “mace mai kyau ba” amma fa ranar da na fara ganin ki a duniya na tabbatar da abunda ake nufi da kalmar kyau ga mace.

Kalaman Soyayya text Message

Karanta: ALAMOMIN SOYAYYAR GASKIYA


Wasu lokutan, nakan yi tinanin rayuwa ta babu ke aciki, babu komai a cikin ta face damuwa da bakin ciki. Ina matukar son ki.


Yana iya kasancewa ni ba irin saurayin da kike so bane, amma ina tabbatar maki da cewa zan iya bada rayuwa ta dan farin cikin ki matukar hakan zai sa kisan matsayin ki a zuciya ta.

Karanta: YADDA AKE FARA SOYAYYA DA BUDURWA

Muna fada a tsakanin mu, muna samun saba ni, amma hakan bai taba rage son da nake maki a zuciya ta ba. In aka tambaye ni wannan wani irin soyayya ce, nace nayi mata lakabi da zanen kaddara.


A lokacin da mutane suke ganin raunin ki, ni babu abinda nake gani face mace mai cike da nasara.


Nasan wasu lokutan zaki rinka yin tinani soboda yawan kiran ki danake da sassafe da kuma cikin dare, bakomai yasa nake hakan ba sai dan inaso muryar ki tazamo na farko da zanji duk safiya inna tashi daga bacci kuma tazamo na karshe kafin na kwanta. 


Muryar ki kawai na dauke da sinadarin sanya farin ciki da nishadi a zuciyar kowani dan adam. Shiyasa nake kara godewa ubangiji da ya hadani dake a wannan duniyar da muke ciki.


Wasu suka ce kina da girman kai, wasu kuma jan aji, amma na dauke hakan karya dan kuwa ni nasan baki da girman kai, tsare girman ki ne kawai dan haka ki cigaba.

Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAÆŠUWA

Na fada maki wani abu guda daya? Ki zama mai yawan murmushi a koda yaushe, domin murmushin ki na da matukar kayatarwa.


Farin ciki, annashuwa da kuma nishadin da nake fuskan ta a kullin, ba dan komai bane sai dan nayi nasarar samun ki a zuciya ta. Kaunar ki ta maimaye zuciya ta.


Daga ran da na fara ganin ki nasan cewa ke tawace ni ka dai. Sai dai kuma bakizo lokacin da nake tsammani ba.


Wasu lokutan ji nake kamar ina mafarki dan duk wani damuwa da nake ciki, kina dauke da maganin ta.

Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA

Samun budurwa irin kina da matukar wuya, duk halin da saurayi zai nema a wurin ya’ mace duk nagan su a tare dake. Nayi sa’a matuka.


Sarauniyar rayuwa ta, dafatan kina lafiya? Tin da muka hadu nake ta farin ciki, farin cikin ya kasa boyewa a fuska ta, ji nake kamar anyi mun kyautar aljannah tun a duniya.


Wasu mutanen sunce soyayya tana da dadi ne a farkon haduwa, amma kullin gani nake kamar duk ranar duniya soyayyar ki a gare ni karuwa take.


Bana waka ko kadan, amma zanje na koya dan na rinka rera maki wakokin soyayya masu dadi da sa farin ciki. 


A duk sanda na wayi gari ban gan ki ba ko banji muryar ki ba, wannan ranar cikin bakin ciki nake kasancewa. Ina so ki ringa kasacewa a kusa dani a koda yaushe dan zuciya ta ta samu sauki.

Karanta: YADDA AKE SACE ZUCIYAR MACE

Duk in aka tambaye ni me nakeso a rayuwa, amsar da nake basu itace kasancewa tare dake har tsawon rayuwa ta. Nagode sosai masoyiya ta dan kin kara wa rayuwa ta ma’ana.


Nazamo mai muradin kasancewar ki a rayuwa ta, dan tarayya dake yasa abubuwan alkhairi kawai nake fuskan ta aduk lamarina. Inaso wannan alkhairin da nake gani su cigaba da kasancewa a tare dani.


Aduk sanda nake cikin wani hali da nake bukatar agaji, Allah ya turo sarauniya cike da soyayya ta agaza mun, gaskiya sarauniya irinki nada wahalan samu.


Masoyiya ta, nazama saurayi wanda yasamu babban rabo a duniya dan samun budurwa kamar ki a rayuwa ta. Duk wata rana na rayuwa ta na zuwa da abubuwa na ban mamaki kuma kece silar faruwar hakan.


Duk in akace na misalta irin soyayyar danake maki, kalamai, kwatance, da kuma bayanai basu iya tabbatar da asalin yadda nakeson ki kuma nasan kinsan da hakan.


Baby na, duk wani wahala da damuwa da nake ciki, mantawa nake da ita duk sanda na hadu da ke ko kuma naji muryar ki. 


Masoyiya ta, gara na zauna a cikin zuciyar ki da na kasance a cikin tinanin ki dan zaki iya manta abun da kike tinani cikin sauki, amma kuma duk abunda ke cikin zuciya ya samu wurin zama.

Karanta: HALAYEN-MATA-TA-GARI

Inason ki kuma banson na rabu da ke dan kuwa rayuwa babu ke a cikin ta cike take da bakin ciki da damuwa. Kizama tawa nikadai kinji?


Masoyiya ta, inaso ne kawai na tina maki cewa arayuwa ta kece a farko kuma kece a karshe. Kinzamo mai sani cikin nishadi da farin ciki.


Duk lokacin da idanuna suka kalli fuskar ki, sai naji kamar nazama sarki, in kuma naji muryar ki, sai naji kamar rayuwa ta bani kyautar da banta samun irin ta ba, sawun tafiyar ki kuma abun koyo ne ga wasu yammata.


Yammata adan gari, abokan rayuwa, masu zuwa da abubuwan alkhairi, masu dauke da sinadarin dake magance damuwa da farin ciki, na shaida kuma na gas gata hakan dan na samu farin ciki mai yawa.


Kamar yadda dubbanin taurari ke haskaka samaniya, haka murmushin ki ke haskaka rayuwa ta.


Babbar kwarin gwiwa da na samu a rayuwa ita ce karfafa wa dana samu daga wurin ki. Babu ta inda zan iya biyan ki daya fi na so ki fiye da yadda kika taba jin so a zuciyar ki. Ina godiya sosai.


Kullin tinanin ki cike yake a cikin zuciya ta kuma inason hakan, dan damuwa bai iya zuwa inda nake ba ta dalilin samun ki a rayuwa ta.


  Masoyiya ta, babbar abun farin ciki a rayuwa ta itace natashi da safe tare da tinanin ke tawa ce ni kadai. Hakan ma kawai ya ishe ni farin ciki a rayuwa ta. Ina sonki bil haqqi.


Da zaki san irin farin cikin da nake shiga soboda soyayyyar ki, da kin kara godewa ubangiji soboda wannan babbar kyauta da yayi miki.

Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE

Wasu su kirani mara hankali, wasu suce bansan me nakeyi ba, amma kuma hakan bai dameni ba, dan kyautata maki itace babbar muradi na.


Duk sanda muke tare, jina ke kamar ranar muka fara haduwa, soyayyar da nake maki kara mamaye zuciya ta take fiye da yadda nake tinani.


Ganin da yafi kowani gani a rayuwa ta itace kallon cikin idanun ki naga irin kaunar da kike mun. ke din ta musamman ce a cikin mata.


Samun ki a rayuwa ta tasamo ma rayuwa ta mafita wuce yadda nake tinani, duk abunda na gwada yi a baya da bai samu karbuwa ba, ta dalilin shawarar ki nasami hakan cikin sauki ba tare da nasha wuya ba.


Inda ace zan iya bude maki zuciya ta kiga irin soyayyar dake cike a cikin ta, da kingane cewa duk abunda nafada maki gaskiya ce.


Zuwar ki rayuwa ta tasa na fahimce me ake nufi da so na gaskiya, kaddara, da kuma nasara, domin ke dukkan su ce gare ni ya yar budurwa ta.


So dayawa na kan yi tinanin sunan da zan kira ki da ita, amma kuma sai na kasa samun amsa, dan kuwa duk sunan da zan iya tinani akai ba dace da a kira ki da it aba. Soboda haka kiyi hakuri da sunan da nake kiranki masoyiya ta.


Da irin wannan soyayyar da kike nuna mun, zaki iya kaini koma inane, matukar hakan zai zama silar farin cikin ki kamar yadda kika samar mun da nawa farin cikin.


Farin cikin ki a rayuwa ta abun dubawa ne, dan shi ke samar da nawa farin cikin, dan haka ina da burin naga na faranta maki har karshen rayuwar ki.


Kinzamo mace wacce nake kallo dan nasami karbuwa, na kasance cikin farin ciki mai dorewa tinda na hadu da ke, tinda kika shigo cikin rayuwa ta. Duk wata numfashi da zanyi a duk farkon rana na baki kyautar ta da kuma wacce zanyi a karshe.


Kina da kwarginin da duk in muna tare sai na rasa me zance maki, kalaman baki na gaba daya dauke wa suke kamar ban taba sanin komai ba. Amma kuma hakan farin cikin da nishadi take bani.

Karanta: YADDA-ZAKA-ZAUNA-ZUCIYAR-MACE-CIKIN SAUƘI

Daga randa nafara ganin ki a duniya, murmushin ki ta siye zuciya ta. A ranar na fara tinanin an halicce mu dan mu kasance tare da juna, bazan taba daina tinanin randa zaki zamo tawa ba ni kadai.


Kin kasance irin macen da nake ganin a mafarki na, nake muradin kare rayuwa ta da ita, nakeso dan zuciya ta tasamu sukuni da natsuwa. Kin shigo rayuwa ta asanda nake matukar bukatar ki. Wannan farin ciki da nishadi mai dorewa ma kawai ta ishen ni tunda rayuwata ta inganta.


A cikin wasu mutane, akwai masu kyau da kyawunsu bazai misaltu ba, toh acikin wannan mutanen kece shugaban su, kece sarauniyar su, wannan sarauta taki ce ke kadai. Duk kyawun mace in kina wurin, bata iya nuna kanta dan kuwa zataji kunya.


A duk sanda nake jin yunwa, kalaman ki kawai ke kosar dani. A duk sanda nake jin kishi, murmushin ki ke shayar dani har na koshi. Kinzamo irin budurwan da nake bukata.


Akwai wata sirri dana boye maki banfada maki ba, wannan sirrin itace bake bace mafi soyuwa a cikin zuciyata ba. Kinsan meyasa? Amsar itace mutun na iya gundura da abun da yake so soboda zai iya samun wani. Amma ke, daya ce tak wacce babu irin ta a rayuwa ta. Namaki mazauni a cikin zuciya ta wacce babu abunda zai iya kusantar ki a cikin ta.


Ban taba haduwa da budurwan da ta nuna mun so kamar yadda kika nuna mun ba. Wacce take girmama ni tare da mutunta ni da kuma sanin ya kamata kamar ki. Ina godiya da wannan abun alkhairin.


Babu wani abu da zai iya dakatar dani daga tinanin ki a duk sanda nake zaune nikadai ba tare da ke ba. Kuma ina mai tabbatar maki babu wanda zai iya maye gurbin ki a cikin zuciya ta.

Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA

Acikin wannan duniyar, na fahimci babu wata zuciya data dace da zama na kamar taki zuciyar, shiyasa banda wani mafi kusanci aiki danake so da ya wuci na kyautata wa zuciyar dake sani farin ciki da nishadi.


Gani nake kamar ban fara rayuwa ba, saida na hadu da ke, haduwa dake yaba wa rayuwa ta ma’ana da kuma bani duk wani kwarin gwiwa na kasancewa a raye tare da ke a cikin ta.


Son ki bashi bane rauni na kamar yadda wasu ke cewa, soyayya dake itace karfi da kwarin gwiwa da na samu, yanzu ina iya hanyar gobe na soboda samun ki a rayuwa ta.


Bansan da wani irin kalamai zanyi amfani na yabe ki ba, dan kuwa yabon ki abu ne da bazai yuba sai anshirya masa. Murmushin ki kawai na iya warkar da ciwon zuciya.


Duk abun da ya faru gobe ko anan gaba, inaso ki sani cewa kina cikin rayuwa ta dari bisa dari kuma babu abunda zai iya chanja hakan. Ina sonki yar budurwa ta.


Wasu sukan fadi cewa soyayya nada iya ka, amma gaskiya niban yarda da hakan ba. Dan ni banga wani iya ka tsakanina dake ba. Hakan fadar su ce kawai.


Bantaba kokwanto akan soyayyar da kike mun ba, dan hakan bata wa kaina lokaci ne akan al’amarin da na riga nasan gaskiyar ta. Yar’ budurwa ta, kiyi mun alkawarin bazaki guje niba.


A duk sanda na ganki sai zuciya ta ta buga da sauri, a duk sanda kuma na rike hannun ki, sai naji rayuwa ta tasami salama da natsuwa. Dama haka soyayya da budurwa irin ki ke da dadi. ina kika boye duk wannan tsawon lokacin da bamu hadu ba?


Gaa zuciya ta nan nabaki kyauta, kiyi yadda zaki yi da ita, matukar hakan zai saka ki cikin farin ciki, dan da hakan ne zan iya biyan ki irin farin cikin da kika zo mun dashi.


In aka tambaye ni na misalta kyawun ki da kalamai hudu, amsa ta ita ce “tauraruwa mai haskaka samaniya” 


Soyayyar da nake maki yau tafi ta jiya kamar yadda tafi ta shekaran jiya, kuma haka zalika, ta gobe dole tafi ta yau. Wannan alkawari ce na daukan ma kaina.


A misali yanzu a tambaye ni menene abu guda daya da yake tabbas a cikin zuciya ta, amsar da zan basu ita ce soyayyar ki.


Bama nika dai ba, gidan mu, abokaina, yan uwana dana basu labarin ki duk sun yaba da halin ki kuma sun mana fatan Allah ya bar mu tare.


Abokai da yan uwa, sun tambayan meyasa nake tare dake, kin san me nace masu? Mace kyakkyawa, mai ilmi, mai sanin kimar mutane, mai ladabi da biyayya burin kowani saurayi ne, amma hakan na wahalan samu a gun mace daya, amma sarauniyata ta rabauta da dukkan halayen nan dana lissafo, gaskiya kam nima na rabauta.


Na kasance saurayi mai rauni a cikin lamura na, amma a dalilin samun ki a rayuwa ta, raunin da nake fama dashi ya bace dan zuciya ta ba gun zaman shi bane. Ina son ki.


Yammata yanzu tinda dare yayi, bazamu iya haduwa ba kuma, bara nakoma gefe nayi mafarkin lokutan da muka yi tare kafin mukara haduwa nabaki labari.


Kinsa rayuwa ta ta inganta fiye da yadda nake zato, farin ciki fiye da yadda na nema a gurin ki, nishadi fiye da yadda nayi kokarin samu, ke ce irin macen da duk saurayi kenema, irin budurwar da iyaye ke fatar su aura ma yaran su, nidai na godewa ubangiji da samun ki.

Karanta: YADDA-AKE-SOYAYYA-DA-QARAMAR-YARINYA

 wasu samarin cewa suke sun sami uwar ya’yansu idan suka samu abokiyar zama, amma ni nasami abokiyar rayuwa ta, na sami aminiya wacce zan iya kawowa kuka na, wacce zan nemi shawarar ta inna shiga damuwa , babu abunda ya raje kuma da zan nema.


Masoyiya ta, kin shigo cikin rayuwa ta kin mai da ni mutun na kwarai. Nagode da kasancewar ki a rayuwa ta da kuma bani damar soyayya dake.


Ban taba zaton rayuwa zata bani aminiya kamar ki ba, amma gashi kinzamo aminiya ta kuma me sani farin ciki da nishadi wanda ba kowani saurayi ke samun hakan ba a wurin budurwan sa.


A duk sanda nayi nasarar kallon cikin idanun ki, babu abunda nake gani face zallar so da kuma haske mai haskaka zuciya. Shiyasa nake matukar kishi a kan ki , ba lale ki fahimci hakan a yanzu ba amma zaki fahimta ahankali.


Banson meyasa duk inna tashi yabon ki nake rasa mene ne zance ba, wasu lokutan sai naji kamar bankai matsayin samun budurwa kamar ki ba, amma kuma soyayyar ki ta share mun wannan kokwanton.


Gaba daya nashiga rudani, wai meyasa duk abunda nake tinani a cikin zuciya ta ke zamo wa kyautar da kike tafe dashi? Wannan abun mamaki ne sosai. Amma soyayya ce bakomai ba.


Kina son sanin ranar da take tarihi wacce bazan taba mantawa ba? Wannan ranar ba kowacce bace sai randa idanuna suka fara kallon kyakkyawar fuskar ki, kunnuwa na suka fara jin muryar ki mai dadi, da kuma randa zuciya ta tafara samun natsuwa acikin ta soboda ke.


Masoyiya ta kina da matukar kyau. Kyawun ki ya wuce misaltawa. Bazan taba manta irin basirar da Allah yayi maki wanda hakan ya taimaka mun a cikin lamurana. Mutuncin da kike da ita kawai ta ishe ni jindadi. Nayi sa’ar samun budurwa irin ki.


Babbar kyauta da nake samu a rayuwa ta kullin ita ce kallon fuskar ki a yayin da kike murmushi. Wannan babbar kyautar ba abun mantawa bane.


Baki san irin mahimmancin da muryar ki ke da shi a cikin rayuwa ta ba, duk damuwar da nake ciki, muryarki kawai nada wannan maganin. Sinadarin dake share bakin ciki da damuwa na kulle cikin muryar ki.


Kinzo cikin rayuwa ta kin cike duk lungu da sako dake cikin zuciya ta, soyayyar ki tazamo mun da farin ciki. Kuma wannan farin cikin zai cigaba da dorewa matukar ina numfashi.


Har karshen rayuwa ta, zan cigaba da samar maki da farin ciki da jindadi kamar yadda nima nasamu daga gare ki. zanyi iya bakin kokarina na kaudar maki da bakin ciki da damuwa kamar yadda kika kaudar mun da nawa.


Masoyiya ta, ina matukar kewar ki, wasu lokutan bamu kusa da juna, amma ji nake kamar gaki a gaba na kuma hakan kwantar mun yake da hankali. Banso ina kewar ki bansan meyasa ba.


Duk sanda nayi wuni daya tak ba tare da naji muryar ki ba kona ganki ba, a wannan rana da bakin ciki nake wuni. Wasu lokutan har kokarin manta damuwa na nake amma bai yuwa dan ke ce silar farin ciki a rayuwa ta.

Karanta: HANYOYI-GOMA-10-DA-AKE-SACE-ZUCIYAR-MACE

Masana soyayya suka ce inka sami mace mai sonka da zuciyar ta, ka gama dacewa, da farko dai banyarda ba, na dauka duk karyar su ce. Amma yanzu na fahimce cewa samun mace irin ki, cikar buri ce ga duk wanda yasamu irin sarauniya ta. Kamar yadda na rabauta da samu.


Duk inna fito daga daki duk safiya sai na kalli sama, babu abunda da nake gani face murmushin ki mai matukar kayatar wa. Ki kasance mai yawan murmushi kinji abar kauna ta.


Bazan taba manta randa nafara ganin ki ba, ranar nafara sanin me ake nufi da kyau, nayi kokarin tunkarar ki a wannan ranar amma hakan bai yuba, abokaina sukace ke ba irin wacce zata so saurayi kamar ni bace. Amma kuma gashi muna tare. Hakan ma babbar rabo ce a guri na.


Akace sirrin abinci mai dadi sai mace kyakkyawa, mabuyan farin ciki da jindadi, sai mace mai cike da far’a da sanin yakamata kuma na yarda da hakan dan duk wannan alamomin na gansu a tare da dake. Bansan da wani kalma zan iya misalta kyawun ki ba.


Kasancewar ki a kusa dani da kuma soyayyar ki dake zuciya ta yasa na fara cinma duk buri kana. Bantaba danasanin samun ki a rayuwa ta ba. Mace mai irin zuciyar ki basu da yawa. Nagode sosai da wannan dawainiyan da kika dauka nawa.


Kin shigo cikin rayuwa ta tare da alkhairi, jindadi, farin ciki wanda hakan ya kasance abunda nake nema kafin na sameki. Nasan bazaki san irin taimakon da kika ma rayuwa ta ba. Bazan taba mantawa da wannan farin cikin ba ko da ace bamu tare da juna kuma. Ina sonki baby na.


Kamar yadda mutum bazai iya rayuwa ba tare da iska ba, kamar yadda shuka bazata iya rayuwa ba babu rana, ni bazan iya rayuwa ba babu ke acikin ta. Kizamo tawa ni kadai. Silar farin ciki na ba kowa bace sai sarauniyar rayuwa ta.


Matukar ina cikin rayuwar ki, na maki alkawarin bazaki kara shiga cikin damuwa ba, ko bakin ciki dan ta haka ne kawai zan iya biyan ki nishadin da kika shigo rayuwa ta da ita.


Banga amfanin na kasance cikin farin ciki a lokacin da abar kauna ta ke cikin damuwa ba. Hakan ba adalci ne bane. Farin cikin ki ce ke samar da nawa farin cikin. Ina kewar ki sosai.


Duk da bamu dade da haduwa ba, amma jinake kamar tinda aka haife ni na sanki, kin kasance baki son ganin fushi ko kadan a fuska ta. Na kasance na daban a cikin abokaina, kuma ba kowa bace silar sai ke.


Ina sonki, nayi tinanin wannan kalmar ke nuna zahirin soyayya amma kin nuna mun abunda soyayya ke nufi, dan kuwa kamar yadda ake shan zuma, haka nasha ta a gurin ki.


Bantaba tinanin zantaba yin kishi akan wata mace ba, sai gashi yau nine ke kishi akan sarauniya ta, ban kaunar naga wani yana kallon ki ko yana miki magana. Hakan nasani cikin damuwa.

Karanta: YADDA-AKE-YIWA-MAZA-SHAGWABA

Gidanmu da yawan cin abinci aka sanni kafin nasanki. Amma yanzu bahaka nake ba. Soyayyar ki tasa yanzu abinci ba matsala ta bace, kwanciyar hankalina lafiyar ki. Banso kina shiga damuwa.


Masoyiya ta, gani nan zuwa wajen ki. Akan hanya ta babu abunda zanyi face na kulle idanuna dan banso naga wata bake ba. Idanuna ke suke muradin gani, muryar ki suke muradin ji. Dan haka sai nazo.


Masoyiya ta, nazo maki da wani albishir mai dadi, mahaifina ya tambaye ni mai nake so a duniya? Nace masa farin cikin ki ce muradina kuma yayi mana fatan nasara, bakomai yasa yace hakan ba sai dan halin ki. Burina ya fara cika. Har na kosa kizama tawa ni kadai.

Post a Comment

0 Comments