Header Ads Widget

YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HADUWA

 YADDA SAURAYI ZAI FARA SOYAYYA DA BUDURWA KARON FARKO


Soyayya halitta ce da take da Matuƙar tasiri a rayuwa ɗan Adam jinsin Mace da Namiji baki ɗayansu.

Akwai matuƙar ban mamaki yadda masoya ke kulluwa da junansu, har zaku ga idan basuga juna ba ko basu suji muryar juna ba sai kaga kowanne daga cikinsu ya kasa samun natsuwa.

Wannan wata muhummiyar shaƙuwa ce da take kunshe da tarin dalilai irin nata, zaka ga sau da yawa wasu tarin masoyan a rayuwarsu ta soyayya suna yin soyayyar su amman sai dai shakuwar tasu bata kai na wasu masoyan ba.

Karanta: FARILLAN SOYAYYA GUDA 7

A yau zanyi bayani ne akan yadda Saurayi zai tunkari budurwa kai tsaye da maganar soyayya ko kuma yadda zai bayyana soayayyarsa ga wacce yake so bz tare da yaji tsoro ko kuma wani fargaba a cikin zuciyarsa ba.

Amma kafin nan akwai wata nasiha da nake son bawa dan uwa na namiji wanda yake soyayya ko kuma kai da kake shirin fara soyayya domin kaucewa wasu abubuwan da idan aka fada cikin su a duniyar soyayya komai na iya faruwa.

Akwai hanyoyi masu tarin yawa da zaka iya yin amfani da su wajen sace zuciyar wacce kake so Waɗanda ma wasu daga ciki ba sai ka tunkari budurwa kai tsaye ba, ita da kanta tana iya zuwa dakanta ta faɗa maka tana sonka duk da dai su mata an sansu da matuƙar kunya.

Hirar Soyayya Farkon haduwa

Karanta: KUSKUREN DA SUKE BATA SOYAYYA

Amfani da kalaman soyayya masu daɗi da matukar inganci a lokacin da kake gwagwarmayar neman soyayyar mace ko kuma ince neman amincewar zuciyar ta.

Kasance mai lissafi hadi da tabbatar da cewa kana tauna duk wata kalma da zata dinga fitowa daga bakinka kafin ka furta ta izuwa ga wacce kake so.

Tauna duk wata Magana kafin a furta ta yana da matukar muhimmanci domin kuwa bahushe yana cewa Magana zarar bunu ce idan har ta fita to a dawo da ita.

Idan har ya zamana kullum kana amayar da kalamai marasa dadi to tabbas zaka ci karo da babbar matsala a rayuwarka ta soyayya gabadaya.

Kada ka sance mai tsauri da takura mata akan ra’ayoyinka domin hakan na iya sawa ta dinga kosawa da kai kuma ta daina marmarin yin hira dakai.

Kuma kayi kokarin zama mai yarda da duk abin da ta zo da shi a ko da yaushe, idan ya kama nay i mata gyara ne to sai ka yishi cikin siyasa da wasa yadda ita zata ba tare da taji bab dadi ba.

Karanta: HANYOYIN-SAMUN-YADDAR-MACE

A kullum ka dinga nuna mata cewa tafi duk wata mace kyau a wajenka, kuma duk lokacin da kukayi waya ko kuma kuna tare ka dinga kokarin nuna mata cewa komai nata daban ne da na sauran mata.

Ka nuna mata yadda muryarta tafi muryar duk wata mace dadi wasu lokutan har da karya ka kara dashi amar irinsu ‘’baby idan har banji muryarki ba bana iya yin barci kuma bana iya cin abinci, wannan zai iya sanyata taji cewa ita tamkar sarauniya ce a wajenka.

Ita soayyaya dole sai da kyauta ka dinga samun kana yi mata koda kuwa tafi karfin abin da zaka bata, domin kuwa tsada ko girman kyautan da zaka bata bashi bane zai saka taji dadin kyautar ba, kyauta ko wacce iri ce wanda zai nunna mata irin muhummancin da take dashi a wajenka.

Kai indai yarinaya tana yimaka soyayya irin na gaskiya ko kanyen mangoro katsinka kabata shi a matsayin flower soyayya wallahi za ta amsa da hannu bi-biyu kuma tayi masa adanawar da bakayi tsammani ba.

Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAƊUWA

Idan zaka iya kuma kana da hali duk sand aka tashi zuwa wajenta hira ka dan dinga rike mata wani abu ko yaya yake, amman fah kada kayi kuskuren sabar mata kudi masu yawa ko kuma siyo mata abubuwa masu tsada domin gudun kada ta mayar dakai na’urar ciran kudi(ATM).

Idan kana Buƙatar mace ta soka sosai kada ka kasance mai tsananin kishi da yawa mata basa son maza masu tsananin kishi dayawa, kuma kada ka zaƙe wajen takura mata akan abubuwan da basu kai a damu dasu ba.

Hakuri da kau da kai daga laifin da tayi maka yana kara sanya mace taji matukar sonka ga kuma kwarjini da zaka kara samu a idanuwanta, kuma ko da wani yakawo mata gulmarka ita da kanta zata wanke ka.

Idan kuna soyayya da mace yazama dole watarana zaku sami matsala tayi maka laifi, hakurin da zaka yi da kau da kai duk da cewa zaka iya daukan mataki akai zai sa ta kara matukar sonta a zuciyarka.


YANZU ZAMUJE KAN YADDA SAURAYI ZAI BAYYANA SOYAYYARSA GA BUDURWA A RANAR FARKO.

Dazaran kaga budurwar da kake so ko kuma wacce ka dade kana sonta kada ka tsaya kayi kasa a gwuiwa.

Karanta: YADDA-AKE-CHATTING-DA-BUDURWA

Idan a taron jama’a ne kada ka tsayar da ita domin ba zata baka wata dam aba tayin Magana da it aba, ka kasance cikin tsabta sannan kayi dressin mai kyau irin wacce ake yayi ko kuma kayi salo irin naka wadda ka saba da ita.

Sai ka bi ta sannu a hankali a baya kuma lallai ka gyara takunka ta yadda ko da ta juyo bata gan cewa ita kake bibiya ba idan kaga ankai wani wajen da yake a natse babu hayaniyar kowa da komai a wajen sai kayi mata sallama.


Ga Misali A Kasa:

Assalamu’alaikum …ita kuma zata amsa tare da kallon ka da gefen ido

...Yan mata dan Allah idan bara ki damu ba ina so kidan bani mintuna biyu ko uku cikin lokacinki. (zata nemi tayi maka musu wataqila ma tafaɗa maka sauri take aiko ta akayi ko kuma bata son bata lokaci ne), amman dai kai kada kadamu.

: Dan Allah kiyi hakuri wata yar Yar sako ne da wani aboki nay a bani in baki don Allah (cikin sauri zaka ga ta nemi sanin waye daga cikin abokanka sannan kuma wacce iriyar sako ce aka baka ka bata)

Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA

To kai kuma sai ka sami nutsuwa ka bayyana mata cewa Abokin nan naka ya kamu da matukar kaunarta da dadewa ma ba wai nan kusa bah kawai dai yadda zaiyi yazo ya tunkare ta ne ya fada mata shine ya kasa.

To amman yau dai a matsayinka na babban abokinsa kazoo ka bayyana mata komai a yi ta ta kare domin idan ka barin abokinka zai ci gaba da cutar da kansa ne wanda kuma haka na iya haifarv da watab babbar damuwar da ka iya sanadin nakasa ko kuma ma rasa rayuwarsa gabadaya.

Da zaran taji haka daga gareka cikin hanzari zata nemi tasan wanene wannan abokin naka kuwa ya sunanshi ma tukunna, kai kuma nan take dama kanan da tafe da wayarka dauke da hotonka a fuskar wayar kawai sai ka dauka ka nuna mata hotonka tare.

Karanta: YADDA-ZA-KAYI-IDAN-MACE-BATA-KARBI-SOYAYYAR-KA-BA

Zatayi mamaki tare da jefo maka da tambayar cewa wannan ai hotonka nake gani, kai kuma sai ka faɗa mata cewa eh daman kaine abokin naka, daman ba wani bane kaine ka tsinci kanka a duk wannan halin da zayyano mata.

Mamaki, kunya tattare da ban dariya zasu kewayata Insha Allahu daganan kuma soyayya ta kullu kenan.



Post a Comment

0 Comments