Jerin Yarukan Nigeria: Yare Nawane a Najeriya?
Najeriya kasa ce mai ɗunbun yawan mutane fiye da miliyan dari biyu (200+ million). Kuma mutanen nan ba yaren su ɗaya ba. Akwai yaruka dayawa da ake yi a Najeriya. Wasu yaren na wasu kasa ne kamar Turanci, Larabci, da kuma Faransa.
Wasu yaren kuma ta muce na yan Najeriya. A wannan shafi, zan bayyana maku yare nawane a Najeriya. Zan kuma lissafa maku manyan yarukan Najeriya guda goma da ake fi yinsu.
Yare Nawane a Najeriya?
Yarukan Najeriya suna da yawa. Bisa lissafin da akayi, akwai yaruka akalla sun kai 525 (over 525 languages) a Najeriya. A cikin su, akwai manyan yaren da akeyi a jaha sun fi daya. Wasu kuma kai wani karamar hukuma (Local Government) kawai ake yin sa. A cikin lissafi yaruka fiye da 500 dinnan ba’a sa turanci ba dan aronsa mukayi amma tafi ko wani yare yawan masu yin sa a Najeriya.
Karanta: ILLOLIN CIN NAMAN DABBOBIN DA AKA HANA CI
Jerin Manyan Yarukan Najeriya
A wannan ban gare, zamu tattauna akan manyan yarukan da aka fi yinsu da sanin su a Najeriya. Kamar yanda muka fada a baya, wasu yaran ana yin su a jahohi da yawa. Wasu kuma akalla akwai mutane million da suka iya su. sune manyan yarukan Najeriya. Bazamu yi magana akan Yare wa inda muta ne daya basu yin sa ba kamar wanda kayi a karamar hukuma daya kawai ake yin su.
1. Hausa
Harshe na farko da aka fi amfani da ita shine harshen Hausa. Akalla akwai mutane miliyan hamsin (50+ million) dasu ke amfani da shi idan za a kirga harda wa inda ba Hausawa ba da suka iya yaren Hausa. Daga cikin su akwai kabilun Fulani da kuma duk wani kabila tunda ba jahar da zaka je a Najeriya baka tarar anyi Hausa ko dan yaya ba. Idan za’ayi maganar Jahohin da aka fi yinsa, toh suna da yawa.
Akwai Kano, Katsina, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Bauchi, Adamawa, Gombe, Borno, Yobe, da Taraba. Akwai masu yin sa da yawa a kuma Niger, Plateau, Nasarawa da sauran Jahohi a Arewa ta tsakiya (north central).
2. Yarbanci (Yoruba)
Yaruba wato Yarbanci a Hausance harshen ne a Najeriya da akalla mutane fiye da miliyan arbain da biyu (42+ million) suke amfani dashi idan zaka hada harda wainda ba yarbawa ba da suke yin yaren. Amfi yin sa ne a kudu maso yamman Najeriya (south west Nigeria). Gaba dayan jahohin dake kudu maso yamman Najeriya garin Yarbawa ne. Jahohin da akafi yin yarbanci sune Lagos, Osun, Ogun, Ondo, Oyo, and Etiki. Ban da wainan Jahohi na kudu maso yamma, akwai yarbawa da dan yawan su a Arewa ta tsakiya kamar Jahan Kwara da wanni bangaren Jahar Kogi.
Karanta: YADDA ZA KAYI IDAN MACE TAQI KARBAN SOYAYYAR KA
3. Igbo
Hausa bata da sunan yaran Igbo kamar yadda take da na Yarbanci. Amma Igbo shima wani mahinmin yare ne a Najeriya. Shine na ukun wazobia – Bia na nufin zo a yaren Igbo. Yaren Igbo shine yaren Inyamirai. Akalla akwai mutane miliyan talatin da hudu (34+ million) da suka iya yaren Igbo idan aka hada da wainda ba inyamurai ba da suka iya yaren. Amfi yin yaren Igbo a garin inyamurai. Jahohin da ake yin yaren igbo sune Enugu, Abia, Anambra, Ebonyi, da Imo. Akwai inyamurai a wasu jahohin kudu maso kudu (South South).
4. Fulfulde
Fulfulde shine yaren fulani. Mafi yawan mutane suna ma fulani kallon Hausawa. Amma ba haka yake ba. Hausawa suna yaren hausa, Fulani na yaren fulani wato fulfulde. Akalla an kimata wai akwai mutane miliyan sha biyar (15 million) da suka iya fulatanci wato fulfulde a Najeriya. Mafi yawan wainnan Fulani ne su. Amma akwai Hausawa wainda suka hada alaka da Fulani da suka iya yaren da yawa. Jahohin da akeyi fulatanci su ne Adamawa, Gombe, Bauchi, Katsina, Yobe, Kebbi, Taraba, da Zamfara.
5. Tiv
Yaren tiv yana daga cikin harsunan da ake fi amfani dasu a Najeriya. Yawannacin masu yin yaren Tiv yan yaren da – Kamar yadda Fulfulde yake. A yansu, akwai akalla mutane miliyan sha biyar (15 million) da suke amfani da wannan yaren da magana. Yaren Tiv ana yin sa ne a Jahar Taraba da Benue. Koh a Jahar Taraba da Benue, ana yin tane a karamar hukumar da mutanen yaren suke. Yawwan mutanen da suke yin Fulfulde kusan daya ne da na Tiv.
6. Kanuri
Kanuri shima wani yare ne a Najeriya wanda mutane da yawa suka iya ta. Wasu mutanen yawance yan kudu sana zatan yan Kanuri Hausawa ne. Amma Kanuri yare ne mai zama kanta. Akima ni, akwai mutane fiye da miliyan goma (10 million) da suke amfani da wannan yaren. Yawanci dai kaskiya yawancin masu yin yaren Kanuri Kanuraine ko kuma wainda da suka zauna da su. Harshen Kanuri amfi yin sa ne a Jahar Borno da kuma wani yanki a Jahar Niger.
Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA
7. Ijo (Ijaw)
Amfi sannin harshen Ijo da Ijaw a Najeriya amma Hausawa na kiran yaren Ijo. Wannan yaren shine yaren Shugaban Kasa Nada Goodluck Jonathan. Yaren shine shahararan yaren da ake fi sani a kudu maso kudu (south south) a Najeriya. A Najeriya kuwa, shine na bakwai. Akalla akwai mutane miliyan uku (3 million) da suke yin yaren nan. Yaren Ijo anayin shi ne a ban garen Najeriya da ake kira Niger Delta. Jahohin da ake yin shi a wannan bangare na Niger Delta sune Bayelsa, Delta, da kuma Rivers.
8. Edo
Edo wani yare ne wanda mutane Edo ko Benin suke yi. Wannan yaren anfi yin sa ne a jahar Edo wanda yake Kudu maso Kudu a Najeriya. Kamar yanda kuka gani bayan Hausa, Yarbanci, da kuma Igbo, shima Edo ba a yin sa a gari da yawa. A Jahar Edo kawai ake yin sa. Kuma mutanen da ke yin sa suna da dan yawa tunda sun kai mutane mililyan biyu (2 million). Wannan yaren shine yare na takwas (8) in dai za’a duba yawan wainda suke yin sa a Najeriya.
9. Annang
Kamar yaren Edo, shi Annang anayin sa ne a kudu maso kudu a Jahar Akwa Ibom. Ana yin yaren ne a cikin Karam hukuma gida takwas (8) cikin hukumomi talatin da daya (31) da suke Jahar. Akwai mutane akalla miliyan daya da suke yin wannan yare. Tare da Edo da Ijo, Annang ma yana cikin yarukan da suke wannan shafin da suke daga kudu maso kudu a Najeriya.
10. Igala
Akwai yare wanda ake kira Igara (gara) akwai kuma Igala. Wanda muke nufi anan shine Igala. Igala wani yare ne da ake fi yi a Jihar Kogi. Mutanen Igala sunfi ko wani yare yawa a Kogi. Yaren akwai mutane akalla miliyan daya (1 million) da suke yin sa a Najeriya. Akwai yan kwaranin su a Anambra, banda Kogi amma sun fi yawa a Kogi.
Karanta: SIRRINKA 21 DAKE SAKA SOYAYYA KARFI DA JIMAWA
Sauran Yarukan Da Ake Yi a Najeriya:
How many languages are spoken in Nigeria? What is the official language of Nigeria? Where do the languages spoken in Nigeria originate from?
• Abanyom
• Abon
• Abua
• Abureni
• Achipa
• Adim
• Aduge
• Adun
• Afade
• Afo
• Afrikaans
• Afrike
• Ajawa
• Akaju-Ndem
• Akweya-Yachi
• Alago
• Amo
• Anaguta
• Anang
• Angas
• Ankwei
• Arabic
• Anyima
• Arum
• Attakar
• Auyoka
• Awori
• Ayu
• Babur
• Bachama
• Bachere
• Bada
• Bade
• Bakulung
• Bali
• Bambora
• Bambuko
• Banda
• Banka
• Bangunji
• Banso
• Bara
• Barke
• Baruba
• Bashiri
• Basa
• Batta
• Baushi
• Baya
• Bekwarra
• Bele
• Betso
• Bette
• Bilei
• Bille
• Bina
• Bini
• Birom
• Bobua
• Boki
• Bokkos
• Boko
• Bole
• Botlere
• Boma
• Bomboro
• Buduma
• Buji
• Buli
• Bunu
• Bura
• Burak
• Burma
• Buru
• Buta
• Bwall
• Bwatiye
• Bwazza
• Challa
• Chama
• Chamba
• Chamo
• Cibak
• Chinine
• Chip
• Chokobo
• Chukkol
• Cipu
• Daba
• Dadiya
• Daka
• Dakarkari
• Danda
• Dangsa
• Daza
• Degema
• Deno
• Dghwede
• Diba
• Doemak
• Duguri
• Duka
• Duma
• Ebana
• Ebirra
• Ebu
• Efik
• Egbema
• Eggon
• Egun
• Ejagham
• Ekajuk
• Eket
• Ekoi
• Ekpeye
• Engenni
• Epie
• English
• Esan
• Etche
• Etolu
• Etsako
• Etung
• Etuno
• Falli
• Fula
• French
• Fyam
• Fyer
• Ga’anda
• Gade
• Galambi
• Gamergu
• Ganawuri
• Gavako
• Gbedde
• Gbo
• Gengle
• Geji
• Gera
• Geruma
• Gingwak
• Gira
• Gizigz
• Goernai
• Gokana
• Gombi
• Gornun
• Gonia
• Gubi
• Gudu
• Gure
• Gurmana
• Gururntum
• Gusu
• Gwa
• Gwamba
• Gwandara
• Gwari
• Gwom
• Gwoza
• Gyem
• Hausa
• Humono
• Holma
• Hona
• Hyam
• Ibeno
• Ibibio
• Ichen
• Idoma
• Igala
• Igbo
• Igede
• Ijaw
• Ijumu
• Ika
• Ikorn
• Irigwe
• Isoko
• Isekiri
• Iyala
• Izere
• Izondjo
• Jahuna
• Jaku
• Jara
• Jere
• Jero
• Jibu
• Jidda-Abu
• Jimbin
• Jirai
• Jju
• Jonjo
• Jukun
• Kaba
• Kadara
• Kafanchan
• Kagoro
• Kajuru
• Kaka
• Kamaku
• Kambari
• Kamwe
• Kamo
• Kanakuru
• Kanembu
• Kanikon
• Kantana
• Kanufi
• Kanuri
• Karekare
• Karimjo
• Kariya
• Katab
• Kenern
• Kenton
• Kiballo
• Kilba
• Kirfi
• Koma
• Kona
• Koro
• Kubi
• Kudachano
• Kugama
• Kulere
• Kunini
• Kurama
• Kurdul
• Kushi
• Kuteb
• Kutin
• Kwah
• Kwalla
• Kwami
• Kwanchi
• Kwanka
• Kwaro
• Kwato
• Kyenga
• Laaru
• Lakka
• Lala
• Lama
• Lamja
• Lau
• Ubbo
• Limono
• Lopa
• Longuda
• Mabo
• Mada
• Mama
• Mambilla
• Manchok
• Mandara
• Manga
• Margi
• Matakarn
• Mbembe
• Mbol
• Mbube
• Mbula
• Mbum
• Memyang
• Miango
• Miligili
• Miya
• Mobber
• Montol
• Moruwa
• Muchaila
• Mumuye
• Mundang
• Mupun
• Mushere
• Mwahavul
• Ndoro
• Ngamo
• Ngizim
• Ngweshe
• Ningi
• Ninzam
• Njayi
• Nkim
• Nkum
• Nokere
• Nsukka
• Nunku
• Nupe
• Nyandang
• Obolo
• Ogba
• Ogbia
• Ododop
• Ogori
• Okobo
• Okpamheri
• Olulumo
• Oron
• Owan
• Owe
• Oworo
• Pa’a
• Pai
• Panyam
• Pero
• Pire
• Pkanzom
• Poll
• Polchi Habe
• Pongo
• Potopo
• Pyapun
• Qua
• Rebina
• Reshe
• Rindire
• Rishuwa
• Ron
• Rubu
• Rukuba
• Rumada
• Rumaya
• Sakbe
• Sanga
• Sate
• Saya
• Segidi
• Shanga
• Shangawa
• Shan-Shan
• Shira
• Shomo
• Shuwa
• Sikdi
• Siri
• Srubu
• Sukur
• Sura
• Tangale
• Tarok
• Teme
• Tera
• Teshena
• Tigon
• Tikar
• Tiv
• Tula
• Tur
• Ufia
• Ukelle
• Ukwani
• Uncinda
• Uneme
• Ura
• Urhobo
• Utonkong
• Uvwie
• Uyanga
• Vemgo
• Verre
• Vommi
• Wagga
• Waja
• Waka
• Warja
• Warji
• Wula
• Wurbo
• Wurkun
• Yache
• Yagba
• Yakurr
• Yalla
• Yandang
• Yergan
• Yoruba
• Yott
• Yumu
• Yungur
• Yuom
• Zabara
• Zaranda
• Zarma
• Zayan
• Zul
Daga Ƙarshe
Yaruka goma dana lissafa sune yaren da suka fi yawan mutane masu amfani da su a Najeriya. Amma kamar yadda na fada, yawan yaren Najeria yakai 525 banda Turanci, Larabci, da kuma Faransanci.
0 Comments