Header Ads Widget

MATASHI YA CANJA SUNAN 'YARSA ZUWA NA MAHAIFIYAR SHUGABA TINUBU SABODA SOYAYYAWani matashi mai matsakaicin shekaru a jihar Bauchi, Khamees Darazo, wanda ya kasa boye soyayyar sa ga shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Asabar din da ta gabata ya cika alkawarin da ya dauka lokacin da ya fito fili a hukumance ya canza sunan diyarsa ta farko mai shekaru 2, Hauwa zuwa Abibatu sunan Mahaifiyar Bola Tinubu.Ya bayyana hakan ne a yayin wata walima na musamman da ya shirya tare da abokansa, wanda aka gudanar a dakin taro na Double 4 da ke cikin garin Bauchi, inda ya bayyana cewa matakin shi ne hanyarsa na nuna goyon baya da biyayya ga Shugaba Bola Tinubu.A cewarsa, “Bayyana goyon bayana ga Shugaban kasa ya faro ne a lokacin da na sadaukar da dukkan alawus din NYSC ɗina, a lokacin da na hidimta wa ƙasa a Jihar Gombe, domin karfafa yunkurin yakin neman zaben Shugaban kasa a tunkarar zaben Shugaban kasa na shekarar 2023.Wani fata zaku yi wa Malam Khamees da 'yarsa Abibatu mai sunan Mama?

Post a Comment

0 Comments